Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKalaman batanci na giftawa a shirin siyasar kafafen yada labarai --- NBC

Kalaman batanci na giftawa a shirin siyasar kafafen yada labarai — NBC

Date:

Shehu Usman Salihu

 

Yayin da yan siyasa ke cigaba da gudanar da yakin neman zabensu a fadin kasar nan, hukumar NBC dake kula da kafafen yada labarai ta ce, kalaman batanci na giftawa a shirye shiryen siyasar da kafafen yada labarai ke gabatarwa a Jihar Kano.

 

Da yake jawabi yayin ziyarar da Cibiyar CITAD, mai bunkasa fasahar sadarwa da cigaban alumma takai ofishin NBC a nan Kano. Malam Adamu Salisu Jami’in hukumar ta NBC anan Kano cewa yayi “babban kalubalen da muka fi fuskanta da kafafen yada labarai a wannan lokaci shi ne shirye shiryen siyasa dake dauke da kalaman batanci wanda ka iya tunzura wani bangare na alumma”

 

Adamu Salisu ya kuma bayyana cewa tun da fari sun aike da takardun gargadi ga kafafen yada labarai don tabbatar da dokar hukumar.

 

Ziyarar CITAD na daga wani bangare na yunkurin tabbatar da zaben 2023 dake karatowa ya inganta, karkashin shirin shigar matasa da mata harkokin siyasa.

 

Babban Jami’in cibiyar, Malam Isa Garba ne ya shaidawa Premier Radio cewa makasudin ziyarar ga hukumar shi ne karfafawa don ita ke da ikon tabbatar da doka ga kafafen yada labaran, hadi da jan hanakali akan yanda ya kamata kafafen yada labarai su gudanar da shirye-shiryen su.

 

Daga bisani dukkanin bangarorin biyu sunyi kira ga yan siyasa da ayi siyasa tsaftataciya ba tare da gaba ko tashin hankali ba.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories