Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Thursday, April 11, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKafofin sada zumunta sun samin hawan jini– Tinubu

Kafofin sada zumunta sun samin hawan jini– Tinubu

Date:

Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya sha alwashin daina duba shafukan sada zumunta saboda suna sashi hawan jini.

 

Tinubu, wanda akai-akai ya kan wallafa labarai a kafofin sada zumunta da ke dauke da sunansa, ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta a halin yanzu.

 

A fefen bediyon an gano Tinubu na cewa “Bazan kara karanta kafafen sada zumunta ba saboda basu da aikinyi sai zagi da tsine mun albarka. Idan na karanta, nakan sami hawan jini don haka idan ina son jin wani abu ‘Ya’yana ko ma’aikata na za su duba su bani labari”

 

Sunan Tinubu, wanda ke kan gaba a yakin neman zaben 2023, ya mamaye kafafen sada zumunta biyo bayan tuntuben harshen da yayi yayin da yake karkare jawabinsa a gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a Jos a ranar Talata.

 

Inda ya ambato sunan tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP a lokacin da ya ke kambama jam’iyyarsa ta APC.

 

Hakan dai ya jawo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta yayin da Al’umma da dama suka yi wa dan takarar jam’iyya mai mulki suka cewa bai cancanci zama shugaban kasa ba.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories