Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGobara ta kone mutum uku kurmus a Kabuga

Gobara ta kone mutum uku kurmus a Kabuga

Date:

Mukhtar Yahya Usma

Wata gobara ta da tashi cikin Daren jiya a kafar Kabuga ta yi sanadiyyar hallaka mutu uku.

 

Shaidun gani da ido sun ce wutar ta tashi ne da misalim karfe 10 na dare a layin masallacin juma’a na Yan Azara.

 

A cewarsu gobarar ta kama gidan wani bawan Allah da ke yin haya a gidan ne inda ta kone yaransa biyu da Kuma kanwarsa kurmus.

 

Sabi’u Mustapha guda ne cikin wadanda suka kai dauki don kashe gobarar ya ce sunyi iya kokarinsu cikin daren amma wutar bata mutuba.

 

Ya ce sai da yan kwana kwana mota uku ta kai dauki sannan aka kashe gobarar Amma dai babu
wanda ya yi rai a cikinsu.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories