Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano za ta rushe gidajen da aka gina a karkashin babbar...

Gwamnatin Kano za ta rushe gidajen da aka gina a karkashin babbar hanyar wutar lantarki.

Date:

Gwamnatin Jihar Kano tace bisa bukatar ministan lantarki, akwai yiwuwar ta rushe gidajen da aka gina a karkashin babbar hanyar wutar lantarki.

 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan, yayin da ministan lantarki Engr. Abubakar Aliyu ya kai ziyarar gani da ido na aikin samarwa da kuma inganta wutar lantarki a jihar Kano.

 

Ministan wanda ya kewaya tasoshin rarraba wutar lantarki na Dan Agundi da Rimin Zakara ya koka da yadda gine-ginen da ake yi ba bisa kaida ba a kan hanyoyin lantarki ke kawo cikas a aikin inganta wutar jihar Kano.

 

Wanda kuma hakan ta sa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yace zai duba lamarin rushe gidajen da aka gina a karkashin hanyar babbar hanyar wutar lantarkin.

 

Ministan yace shugaba Muhammadu Buhari ya dukufa wajen mayar da Kano wata babbar cibiya ta rarraba wutar lantarki a Arewacin kasar nan, don haka yace gwamnatin na son kara yawan karfin wutar lantarki da Kano take samu zuwa megawatt dubu 2, karkashin wani shiri tare da hadin gwiwar kamfanin Siemens na kasar Jamus.

 

Yayin ziyarar, Ministan ya zagaya tashar lantarki ta Dan Agundi, inda ya roki gwamnan da ya sa baki domin ganin cewar an kawar da gidajen da suka yi kutse a karkashin layin lantarki musamman daga Kumbotso zuwa Dan Agundi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories