Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGina Gadojin Sama a Jihar Kano Bashi Da Amfani - Bala Gwagwarwa

Gina Gadojin Sama a Jihar Kano Bashi Da Amfani – Bala Gwagwarwa

Date:

Aikin gina gadojin sama a jihar Kano, Gwagwarwa ya kalubalanci Kwankwaso da Ganduje.

 

Shehu Usman Salihu

 

Yayin da yan siyasa ke cigaba da bayyana manufofinsu na zaben 2023 da ke tafe.

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar SDP mai alamar farin doki, Alhaji Bala Muhammad Gwagwarwa, ya jadda da kudirinsa na habbaka harkokin kasuwanci

 

A zantawarsa da wakilin mu Shehu Usman Salihu, Bala Gwagwarwa ya ce, zai bada fifiko ga yan kasuwa masu sana’ar hannu idan ya kai ga ci “Babbar manufar mu shi ne tallafawa yan kasuwa da masu sana’ar hannu da manoma da masu sana’ar sufiri, sai kuma mu waiwayi bangaren ruwan sha, lafiya, ilimi da sauran al’amuran more rayuwa”.

 

A bangaren harkokin raya birane, Bala Muhammad gwagwarwa ya kalubalanci aikin gina kadojin da gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke yi a yanzu da na Sanata Rabiyu Musa Kwankwaso a baya da suka yiwa jihar Kano da cewa “Idan Allah ya tabbatar dani a matsayin gwamnan jihar Kano ba zan ranto kudi na dinga aikin gina gadar da bata da amfani ba, domin kamata yayi ayi amfani da wadanan kudaden wajen gina al’umma”.

 

“A yanzu haka a jihar Kano, mafi akasarin mutane abinda suka fi damuwa shi ne abinci, harkar lafiya, ilimin yara da sauran alámuran yau da kullum”. Inji Bala Muhammad Gwagwarwa.

 

Dan takarrar gwamna jihar Kano a jam’iyar SDP mai alamar farin doki, Bala Muhammad Gwagwarwa ya ce a kasashen da aka cigaba, al’umma ake fara ginawa da harkan kasuwancin su don gogayya da kowa a fadin duniya.

Latest stories

Related stories