Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano ta raba injinan ban ruwa ga mutane 45 yan asalin...

Gwamnatin Kano ta raba injinan ban ruwa ga mutane 45 yan asalin karamar hukumar Kumbotso.

Date:

Gwamnatin Kano ta raba injinan ban ruwa ga mutane 45 yan asalin karamar hukumar Kumbotso.

Injinan ban ruwan na daga kayayyakin jin kai don rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnatin jihar ke ci gaba da rabawa al’ummar Kano.

Da yake bayani kan batun a yau, Jagoran tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Kumbotso, Dr Dan Yaro Ali Yakasai ya bayyanawa wakilinmu Bashir Aminu Panshekara cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da taimakawa talakawan jihar nan.

Ya ce yanzu haka an fito da abinci da sauran kayan da al’ummar Kano za su amfana da su.

ÆŠaya daga wadanda suka samu tallafin, ya godewa Gwamnan Kano tare da fatan É—orewar tallafin.

Gwamnatin Kano, ta bi sawun sauran gwamnatoci kasar nan wajen rage tallafin rage radadin cire tallafin man fetur.

Har yanzu, wasu al’ummar jihar na fatan rabon ya karaso kan su don samun sauÆ™in rayuwa.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...