Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGobara ta hallaka mutum 3, ta kone shaguna 100 a Kano

Gobara ta hallaka mutum 3, ta kone shaguna 100 a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wata gobara da ta tashi kasuwar kayan gwari ta Badume da ke karamar hukumar Bichi ta hallaka mutum uku tare da kone shaguna 100.

 

Rahotannin sun yi nunu da cewa gobarar ta faro ne da ga wani shago da ke tsakiyar kasuwar.

 

A cewar hukumar kashe gobara ta jihar Kano, bayan samun labarinsu ne suka garzaya wurin, don kai dauki.

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusuf ya ce bayan sun isa ne suka iske wata mata da wasu maza biyu sun makale a cikin wutar.

 

Hukumar ta ce ta yi kokarin fito da su ba yadda suke, sai dai daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwarsu.

 

Ya kuma ce kimanin shaguna 100 suka kone, yayin da suka yi kokari suka dakile ci gaba da yaduwar wutar.

 

Ya kara da cewa har yanzu ba a san musammabin tashin wutarba, amma dai ana nan ana gudamar da bincike.

 

Latest stories

Related stories