Saurari premier Radio
40.8 C
Kano
Monday, April 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMusayar kudi: Darajar Naira ta fara dawowa

Musayar kudi: Darajar Naira ta fara dawowa

Date:

Yayin da wa’adin haramta karbar tsaffin kudi da bankin kasa CBN ya sanya ke karatowa, takardar Naira ta fara farfadowa a kasuwannin canji na bayan fage.

 

Shugaban kungiyar yan canjin na kasa wato ABCON, Alhaji Aminu Gwadabe ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Lagos.

 

Ya alakanta hakan da raguwar bukatar takardun kudin na ketare, inda yawancin mabukata canjin suka koma sayen kadarori maimakon sauyin kudi.

 

To sai dai hakan ya haddasa ninkuwar farashin kayayyakin, inda Tan din sobo na naira dubu 500 ya koma miliyan 1.

 

Gwadabe ya kuma ce jita jitar da aka yada kan yuwuwar dakatar da karbar dalolin da aka buga kafin 2021, ta taimaka wajen rage rubdugun da akayi mata.

 

NAN ta rawaito cewa a jiya Laraba, an ci kasuwar dala akan naira 790, sabanin 900 a yammacin juma’ar da ta gabata.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories