Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGidauniyar Bill and Melinda ta tallafawa Najeriya da dala miliyan 2 da...

Gidauniyar Bill and Melinda ta tallafawa Najeriya da dala miliyan 2 da dubu 400

Date:

Najeriya ta sami tallafin dala miliyan 2 da dubu 400 daga gidauniya Melinda da Gates don yaki da matsalar sauyin yanayi.

 

Ministan muhalli, Mohammed Abdullahi ne ya bayyana hakan jiya a Sharm EL Sheik dake kasar Egypt, inda taron sauyin yanayi na bana, wato COP27 ke gudana yanzu haka.

 

Yace za a yi amfani da tallafin gidauniyar mallakin attajirin nan Bill Gates, wajen bunkasa bincike da kuma raya gandun dazuka,a kokarin dakile kwararowar Hamada.

 

Ministan ya bayyana kwarin gwiwar samun wani tallafin na daban daga bankin raya kasashen Turai EDB, wanda ya bayyana sha’awarsa na daukar nauyin wasu ayyuka a kasarnan.

 

Bai bayyana kafatanin nasarorin da aka cimma wajen kulla alaka da kungiyoyi da gwmnatocin duniya ba, amma ya ce Najeriya na cigaba da kulla yarjeniyoyi daban daban.

 

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories