Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn Kashe Kwamandan Yan Bindiga A Kaduna

An Kashe Kwamandan Yan Bindiga A Kaduna

Date:

Jami’an tsaro sun kashe Dogo Maikasuwa, wani shahararren kwamandan ‘yan ta’adda a jihar Kaduna.

 

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan.

 

A cewar sanarwar, Dogo Maikasuwa, wanda aka fi sani da ‘Dogo Maimillion’ ya jagoranci hare-hare da sace-sacen jama’a da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia, da kuma al’ummomin da ke cikin kananan hukumomin Chikun da Kajuru.

 

Bayanan sirri sun tabbatar da cewa, Dogo yakan sanya kakin sojoji ya kuma yi amfani da bindiga kirar AK47 a duk lokacin da yakai hare-haren.

 

“An kuma gano cewa ya jagoranci mabiyansa wajen azabtar da mutanen da suka sace, inda sukan kashe wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin da aka jinkirta bayar da kudin fansa”

 

“Dogo da sauran mabiyansa sun gamu da ajalinsu yayin arangama da sojojin da suka yi masa kwanton-bauna a wani dajin da ke yankin Gengere-Kaso da ke kan iyakar Chikun da Kajuru.

 

A nata bangaren gwamnatin jihar Kaduna ta jinjinawa rundunar sojin bisa namijin kokarin da suke yi domin dakile ta’addanci a fadin jihar.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories