Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaKungiyoyin Farar hula sun bukaci karin kasafin kudin tazarar iyali

Kungiyoyin Farar hula sun bukaci karin kasafin kudin tazarar iyali

Date:

Gamayyar kungiyoyin fararen hula dake fafutukar inganta fannin kiwon lafiya sun bukaci karin kudi a fannin tazarar iyali a kasafin kudin shekarar 2023.

 

Inda suka ce kaso 5.7 cikin dari da aka ware wa tazarar iyali a kasafin kiwon lafiya yayi kadan wajen gudanar da tsarin a fadin kasarnan.

 

Masu fafutukar karkashin jagorancin Usman Muhammad sun yi kira ga majalisar dokoki da su sake duba kan kasafin kudi domin tabbatar da an ware isassun kudi a fannin kiwon lafiya.

 

Usman Muhammad yace “a kasafin kudin da aka ware wa kiwon lafiya yana nuna kowanne dan kasa an ware mishi dubu shida kacal domin kula da lafiyar shi, wanda hakan kwatakwata bai dace ba”

 

Masu fafutukar da suka hada da kungiyoyi masu zaman kan su guda bakwai sun koka kan yadda har yanzu kasar nan bata samar da kudade isassu da zasu wadaci yawan alummar kasar ba duk kuwa da karuwar alumma wanda ke haddasa rashin tsaro da talauci da yawan mace macen mata masu juna biyu.

 

Sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta dauka na baiwa fannin tazarar iyali kashi daya cikin dari na kasafin kudi ta kuma inganta tsarin tazarar iyalin ta hanyar samar da sinadaran tazarar iyali da tallafi da samar da kudaden da za’a tafiyar da fannin.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories