Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan Bindiga sunyi garkuwa da mutane 19 a hanyar Abuja

Yan Bindiga sunyi garkuwa da mutane 19 a hanyar Abuja

Date:

Hafsat Iliyasu Dambo

 

Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya 19 a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Jihar Taraba.

 

Matafiyan da suka hada da mata da kananan yara, dukkansu daga Jihar Taraba, na cikin wata bas din haya samfurin Hummer ne lokacin da suka fada a hannun masu garkuwa da mutane.

 

A daren Juma’a ne dai motar fasinjojin ta fada tarkon ’yan bindigar da suka tare hanya a yankin Eggon da ke Jihar Nasarawa.

 

Daga nan ’yan ta’addan suka yi awon gaba da daukacin mutanen zuwa cikin daji, har da direban motar, sannan suka kawar da motar daga wajen.

 

Mamallakin motar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace maharan sun fara tuntubar iyalan matafiyan suna neman kudin fansa.

 

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Nasarawa, Mai-yaki Muhammad Baba, ya ce suna da labarin abin da ya faru kuma sun tura jami’ansu domin ceto fasinjojin.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories