Dan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fidda-gwani da aka gudanar a faɗin Nijeriya da ƙuri’u miliyan 1,846,370 .
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, shi ne ya zo na biyu da ƙuri’u dubu 504,117.
Sai kuma ɗan kasuwa, Muhammad Hayatudden ya samu ƙuri’u dubu 177,120.
A jawabin sa bayan fitar da sakamakon, Atiku ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen,, inda ya ce akwai dimokuraɗiyya mai ƙarfi a jam’iyyar su ta ADC.
