Shugaban tawagar aikin Hajjin Kano kuma Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya jagoranci wata tawaga domin kai ziyarar barka da Sallah ga alhazan jihar da ke Mina a ƙasar Saudiyya.
Hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na aikin Hajjin Kano, Mustapha Muhammad ya fitar.
Sanarwar ta ce tawagar ta haɗa da Mataimakin Amirul Hajjin kuma Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano tare da Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle.
Da yake jawabi ga alhazan, Amirul Hajjin ya yaba musu bisa yadda suke gudanar da ibadun Hajji cikin tsari, tare da roƙonsu su ci gaba da yiwa Kano da Najeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.
A wani taro daban, Shugaban Hukumar jin daɗin Alhazai ta Kano Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya sanar da cewa Riyal ɗari biyu da gwamnan jihar yayi alƙawarin bawa Alhazan, za’a bawa kowa na sa da zarar sun koma garin Makkah.
Ya kuma tabbatarwa alhazan cewa hukumar sa za ta ci gaba da samar da ayyukan jin daɗi domin tabbatar da walwalarsu a ƙasa mai tsarki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, Tunda farko, manyan malamai da suka haɗa da Sheikh Aminu Daurawa da Sheikh Tijjani Bala Kalarawi da Sheikh Abubakar Kandahar sun gabatar da wa’azi kan muhimmancin Hajji tare da yiwa alhazan addu’ar Allah ya karɓi ibadunsu.
