Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin babbar Sallah na bana, tare da kira ga jama’a da su gudanar da bukukuwa cikin lumana, da jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa lokacin babbar Sallar wata muhimmiyar dama ce ta koyon darussan sadaukarwa, biyayya, haƙuri da kuma tausayi, tare da bukatar al’ummar musulmi da su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a bikin sallar a rayuwarsu ta yau da kullum.
Gwamna Abba ya kuma yi kira ga iyaye da su gargadi yaransu kan gujewa duk wani hali na rashin da’a a lokacin bukukuwan Sallah, yayin da ya roƙi matasa da su kasance masu bin doka tare da baiwa jami’an tsaro haɗin kai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na taya Shugaba Bola Ahmad Tinubu da Mataimakin sa Kashim Shettima da sauran gwamnoni murnar bikin na babbar Sallah fatan gudanar da bikin cikin nasara da farin ciki.
