Majalisar Wakilan Tarayya ta janye kudirin dokar da ta gabatar a baya kan kafa rundunar ’yan sandan jihohi (State Police), inda ta mayar da hankali kan sabon kudirin gyaran kundin tsarin mulki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike mata.
Daga nan ne aka tura kudirin zuwa Kwamitin Majalisar kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki, domin ci gaba da nazari da kuma ɗaukar matakan da suka dace a bangaren dokoki.
Wannan mataki na nufin cewa an dakatar da ci gaba da tsohon kudirin da Majalisar ta gabatar, yayin da ’yan majalisar suka mayar da hankali kan kudirin da bangaren zartarwa (Shugaba Tinubu) ya gabatar.
Ana sa ran kwamitin zai yi cikakken nazari kan muhimman tanade-tanaden kudirin, kafin ya dawo da shi gaban Majalisar domin ci gaba da muhawara da sauran matakan da ake bi kafin ya zama doka.
