Jam’iyyar PDP ta tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na daga cikin jam’iyyun siyasa uku da suka kasa gabatar da sunayen ‘yan takararsu na shugaban ƙasa da mataimaki a shafin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kafin wa’adin da aka ƙayyade ya ƙare.
Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa sauran jam’iyyun biyu da suka gaza kammala wannan aiki su ne APGA da kuma LP ta tsagin Nenadi Usman.
Wata babbar majiya a INEC ta bayyana cewa kusan dukkan sauran jam’iyyun siyasar da aka yi wa rajista sun yi nasarar dora sunayen ’yan takararsu na zaɓen 2027 kafin rufe shafin.
Hukumar INEC ta rufe shafin karɓar sunayen ‘yan takara da ƙarfe 11:59 na daren Talata, 14 ga Yuli, 2026, bayan wa’adin ƙarin lokaci da ta bai wa jam’iyyun siyasa ya ƙare.
Daga cikin jam’iyyun da suka kammala gabatar da sunayensu akwai APC, ADC da NDC. APC ta gabatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Mataimakinsa Kashim Shettima, yayin da ADC ta gabatar da Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi.
Haka kuma, NDC ta gabatar da Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, tare da Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.
Sai dai rahotanni sun ce har yanzu ana fuskantar ruɗani a wasu jihohi kan sunayen ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da aka dora a shafin INEC.
A wani ɓangaren kuma, takaddama kan shugabancin jam’iyyar ADC na ci gaba da ɗaukar hankali duk da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya shafi shugabancin jam’iyyar.
Duk da hakan, binciken ya nuna cewa har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, shafin INEC na ci gaba da nuna sunan tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, a matsayin Shugaban ADC na ƙasa, yayin da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ke matsayin Sakataren Jam’iyyar.
