Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya ce zai gyara Najeriya cikin shekara huɗu idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.
Amaechi ya bayyana haka ne bayan mika takardun tsayawa takararsa a hedikwatar jam’iyyar ADC da ke Abuja, inda ya kuma soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan matsin tattalin arziƙin da ‘yan Najeriya ke ciki.
Ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su zaɓi shugabanni bisa ƙwarewa da ayyukan da suka yi, ba wai saboda yanki ko ƙabila ba.
Tsohon gwamnan jihar Rivers ɗin ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi sauran masu neman shugabancin ƙasa ƙwarewa, yana mai cewa ayyukan da ya yi a jihar Rivers da ma’aikatar sufuri sun nuna yana da ikon kawo sauyi a ƙasar nan.
Amaechi ya kuma zargi gwamnatin APC da jefa ‘yan ƙasar nan cikin wahala sakamakon manufofin tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa zai shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC kai tsaye, sai dai idan an cimma matsayar tsayar da shi a matsayin ɗan takarar bai ɗaya.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027, inda jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa ƙarfi domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
