Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027, inda ya bayyana cewa zai nemi kujerar ne ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).
Ya bayyana hakan ne yayin wani babban gangamin haɗakar jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a Ibadan.
Sanarwar ta Makinde ta ja hankalin dubban magoya baya da masu ruwa da tsaki da kuma abokan siyasarsa, lamarin da masana ke gani a matsayin wani muhimmin mataki a sauye-sauyen siyasa da ke ci gaba da faruwa gabanin babban zaɓe.
Sanarwar tasa dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027, inda masana ke ganin matakin na iya sauya yanayin siyasar ƙasar, musamman a yankin Kudu maso Yamma.
