Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar sojin kasar nan ta musanta sace mutane a hanyar Damaturu

Rundunar sojin kasar nan ta musanta sace mutane a hanyar Damaturu

Date:

Rundunar Sojin-ƙasar nan ta musanta raɗe-raɗin da a ke yi cewa an yi garkuwa da matafiya a kan titin Maiduguri-Damaturu  da yamamcin ranar Asabar.

Premier Radio ta ruwaito kakakin rundunar haɗin gwiwa ta 7 ‘Operation Haɗin Kai’ Ado Isa ne ya musanta hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce zantuttukan da ake yadawa basu da tushe ballantana makama, a don hakan ne ya nemi jama’a da suyi watsi da shi.

“Mun samu rahoton raɗe-raɗin da a ke yaɗawa a kafafen sadarwa ranar Asabar.

“Haka kuma wasu jaridu ma sun buga jita-jitar cewa wai ISWAP sun yi garkuwa da matafiya a Borgozo a Ƙaramar Hukumar Kaga a Borno.

“To wannan jita-jitar ba ta da tushe kuma ana yaɗa ta ne  domin a kushe ƙoƙarin da “Operation Hadin Kai’ ke yi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƴan Boko Haram ne su ka yi yunƙurin tare hanya a yankin Dole/Bari domin su tada hankalin al’umma.

“Dakarun da ke sintiri a wurin ne su ka zo su ka daƙile yunƙurin na su.

“Ba a ɗauke wani matafiyi a ranar Asabar ba, kawai dai aikin ɓatagari da su ke baƙin ciki cewa zaman lafiya na dawowa a arewa-maso-gabas,’ in ji shi.

Ya kuma jaddada ƙoƙarin da rundunar ke yi na kare  matafiya a titin.

Latest stories

An gano cewa Tinubu ya wuce Landan daga birnin Riyadh

Kwanakin shida tin bayan da shugaban kasa Bola Tinubu...

Related stories

An gano cewa Tinubu ya wuce Landan daga birnin Riyadh

Kwanakin shida tin bayan da shugaban kasa Bola Tinubu...