Kasar Saudi Arebiya ta ce dakatar da jigilar jirage daga Najeriya zuwa ƙasar bai shafi aikin Hajjin 2022 ba.
Cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Saudiya a Nijeriya ya fitar ta ce ƙasar Saudiya ba ta da niyyar sokewa, ko hana yan Nijeriya zuwa aikin Hajji.
Duk da cewa Saudiya ta soke Hajji ga ƴan ƙasashen waje a shekaru biyu da su ka gabata, sanarwar ta ce har yanzu ƙasar ba ta fidda matsaya a kan Hajji ba.
“Saudiya na samar da duk wasu tsaruka na yaki da cutar Korona domin kare ƴan ƙasa, baƙi da kuma alhazai.
“Sannan wannan dakatar da jiragen da ga Nijeriya na wucin-gadi ne kuma bai shafi Hajjin 2022 ba.
“Sabo da haka saɓanin yadda a ke ta raɗe-raɗi, Saudiya ba ta soke aikin Hajji ba,” in ji majiyar.
Idan za a iy tunawa dai a ranar Talata ne Maikatar Harkar Sufurin Jirgin Sama ta Saudiya ta dakatar da jirage da ga Nijeriya zuwa ƙasar a wani mataki na daƙile yaɗuwar sabon nau’in korona na Omicron.