Rundunar Sojin-ƙasar nan ta musanta raɗe-raɗin da a ke yi cewa an yi garkuwa da matafiya a kan titin Maiduguri-Damaturu da yamamcin ranar Asabar.
Premier Radio ta ruwaito kakakin rundunar haɗin gwiwa ta 7 ‘Operation Haɗin Kai’ Ado Isa ne ya musanta hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce zantuttukan da ake yadawa basu da tushe ballantana makama, a don hakan ne ya nemi jama’a da suyi watsi da shi.
“Mun samu rahoton raɗe-raɗin da a ke yaɗawa a kafafen sadarwa ranar Asabar.
“Haka kuma wasu jaridu ma sun buga jita-jitar cewa wai ISWAP sun yi garkuwa da matafiya a Borgozo a Ƙaramar Hukumar Kaga a Borno.
“To wannan jita-jitar ba ta da tushe kuma ana yaɗa ta ne domin a kushe ƙoƙarin da “Operation Hadin Kai’ ke yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƴan Boko Haram ne su ka yi yunƙurin tare hanya a yankin Dole/Bari domin su tada hankalin al’umma.
“Dakarun da ke sintiri a wurin ne su ka zo su ka daƙile yunƙurin na su.
“Ba a ɗauke wani matafiyi a ranar Asabar ba, kawai dai aikin ɓatagari da su ke baƙin ciki cewa zaman lafiya na dawowa a arewa-maso-gabas,’ in ji shi.
Ya kuma jaddada ƙoƙarin da rundunar ke yi na kare matafiya a titin.