30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
HomeLabaraiAn gano jaririyar da aka sace daga Neja a Kano

An gano jaririyar da aka sace daga Neja a Kano

Date:

An gano wata jaririyar mai kimanin wata hudu a duniya, da aka sace daga kauyen Daga na Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja, a Jihar Kano.

Premier Radio ta ruwaito mahaifiyar jaririyar, Fatima Kabir, ta ce an sace jaririyarne mai suna Samhat a ranar Juma’ar da ta gabata.

Fatima dai ta garzaya Kano ne ranar Alhamis, lokacin da aka nuna mata wani hoto da ke cigiyar ’yartata a dandalin sada zumunta na Facebook a Jihar Kano.

Wani abokin mijin Fatiman, Ado Musa, a zantawarsa da Daily trust ya ce sai dai murnarsu ta koma ciki ne bayan da Dagacin da aka tsinci yarinyar a yankinsa ya ki yarda ya basu ita.

Ya ce har Hakimin Dakwa, Alhaji Alhassan Musa da kansa ya kira daya daga cikin mutanen da ke kula da lamarin a Kano, amma ya ce sun dauki matakin ne bayan wani shi ma ya yi ikirarin cewa jaririyar ’yarsa ce.

Hakimin na Dakwa dai ya ce tuni ’yan sanda suka shiga lamarin, inda dukkan bangarorin suka amince a yi gwajin kwayar halitta na DNA, don gano hakikanin iyayenta.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...