Premier Radio 102.7 FM
Gwamnatin Kano Kano Labarai

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta bada belin darakta a hukumar kare hakkin mai siyan kayayyaki

Hukumar yakin da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bayar da belin daraktan tabbatar da nagartar kayyaki a hukumar kare hakkin mai sayen kaya ta jihar Kano Malam Bello Alkarya .

Shugaban hukumar Barrister Mahmud Balarabe ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Premier Radio ranar Asabar.

Barrister Mahmud ya ce an bayar da belinsa ne sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita, bayan ya kwashe kwanaki biyu a hukumar.

“An bayar da belinsa sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

“Kuma za a dawo da shi ranar Litinin mai zuwa domin ci gaba da tuhumar da ake yi masa.” A cewarsa.

Hukumar ta kama Alkarya ne a ranar Alhamis din da ta gabata bisa zargin cinhanci da rashawa.

Ko a watannin baya sai da aka kama wani daraktan hukumar da makamancin wannan zargi.

A makon da ya gabata ma sai da hukumar tsaro ta DSS ta tsare shugaban hukumar Janar Idris Bello Dambazau, kan zargin rufe wasu gidajan mai a nan Kano ba bisa ka’ida ba.

A yan kwanakin nan dai mutuncin hukumar na ta zubewa a idon jama’a la’akari da yadda ake ta samun manyanta da laifukan almundahana da kudaden al’umma.

A Wani Labarin...

INEC: Zata rufe yin rijistar katin zabe

Aminu Abdullahi Ibrahim

Babban taron kasa: APC ta fitar da tsarin shugabancin shiya-shiyya

Mukhtar Yahya Usman

Executive order no 10: Me dokar ta ke nufi

Mukhtar Yahya Usman