Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaOmicron: Najeriya ta dakatar da jiragen Saudiyya Burtaniya da Canada shiga kasarta

Omicron: Najeriya ta dakatar da jiragen Saudiyya Burtaniya da Canada shiga kasarta

Date:

Gwamnatin tarayya za ta dakatar da shigowar jirage da ga kasashen Canada da Burtaniya da kuma Saudiyya.

Premier Radio ta ruwaito wannan na zuwa ne a wani mataki na mayar da martani ga kasashen na hana al’ummar kasar nan shiga kasashensu.

Minisatan kula da zirga-zirgar jiragen sama Hadi Sirika ne ya sanar da hakan ranar Lahadi a jihar Lagos.

Dakatarwar za ta fara aiki daga ranar Talata 14 ga Disambar wannan shekara.

Ya ce daukar matakin, martani ne na hana jirage da ga kasar nan shiga kasashensu, biyo bayan bullar sabuwar annobar Covid-19 nau’in Omicron.

Ya ce matukar wadannan kasashen za su dakatar da jirage daga kasar nan shiga kasashensu, babu dalilin da Najeriya za ta kyale nasu jiragen shigo mata kasa dan al’amuran kasuwanci.

“Mun fitar da matsaya kan cewa abune da ba zamu yarda dashi ba, shi yasa muka bada shawarar dakatar da kasashe irinsu Canada Burtaniya da Saudiyya da Argentina.

“Kamar yadda suka yi mana, idan ba za su bar al’ummar kasarmu shiga kasashensu ba, dan me jiragensu za su dinga shigo mana kasa suna daukar fasinja.

“Bai kamata su zo ba, ina tabbatar muku nan da kwanaki uku, Litinin ko Talata, wadannan kasashe za mu hanasu shigowa kasar nan, a cewarsa.

Ya kuma ce za a ci gaba da dakatar da wadannan kasashe, harma duk wata kasa da ta dakatar da Najeriya.

Hadi Sirika ya baiwa al’umma kasar nan hakura, musamman masu shirin zuwa wadannan kasashe, a cewarsa an dauki matakin ne saboda kare martabar ‘yan kasa.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...