40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
HomeLabaraiAddiniMatsalar tsaro: Sarkin Musulmi ya bukaci al’mma su fara alkunutu

Matsalar tsaro: Sarkin Musulmi ya bukaci al’mma su fara alkunutu

Date:

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci al’ummar musulmi su fara alkunutu a kowacce sallar farilla domin neman dauki daga matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.

Premier Radio ta ruwaito wannan na kunshe cikin wata sanarwa da babban Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam Dokta Khalid Aliyu ya fitar ranar Lahadi.

Sarkin musulmin ya kuma bakaci limamai da malaman Islamiyya da na makarantun allo, su dukufa da addu’o’I na musamman.

A cewarsa addu’a ita ce babban makamin mumini, kuma hanya daya tilo da za ta kawo sauki cikin matsalar tsaro.

“Allah madaukakin Sarki shi ne mai rahama mai jinkai, yana bukatar a koma gasheShi in aka shiga halin tsanani da kunci, saboda babu abin da ya fi karfinSa.

“Ga Musulmai, addu’a wata babban makami ce a dukkan halin da muka tsinci kanmu a rayuwa, amma sai dai abin takaici a Najeriya, yanzu mun tsinci kanmu cikin yanayin yawan aikata sabo, cin hanci da rashawa da kuma aikata barna,”.

Sarkin musulmin ya ce komawa ga Allah a yanzu ita ce kadai hanyar da ta rage wa Musulman Najeriya, kasancewar Allah ba Ya rufe kofar karbar tuba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...