Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar da kara rage farashin dizel daga N1,200 zuwa N1,000 duk lita daya a fadin kasar nan.
A baya dai musamman makonannin da suka gabata, lokacin da matatar ta soma aiki, kamfanin yana sayar da farashin dizel a kan naira 1,200 duk lita guda.
Hakan na nufin an yi ragin fiye da kashi 30 cikin 100 daga farashin da ake sayar da dizel din a baya kimanin N1,600 kowace lita.
Matatar ta ce muhimmin ragin da aka yi kan farashin na dizel zai yi tasiri sosai a bangaren tattalin arziki tare da rage hauhawar farashin da ake fuskanta a kasar nan.
Hakazalika Matatar Dangote ta kuma soma gudanar da harkokinta ne da sayar da man jirgi da kuma na dizel.