Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

Kotu a Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

Date:

Wata babbar kotu da ke nan jihar Kano ta dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

Mai shari’a Usman Malam Na’abba ne ya yanke hukuncin bayan karar da Dakta Ibrahim Sa’ad ya shigar a madadin jagororin jam’iyyar biyu a mazaar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.

Mambobin jam’iyyar da aka shigar da karar a madadinsu su hada da mataimakin sakatare, Laminu Sani da mai bai wa APC shawara kan harkokin shari’a, Haladu Gwanjo wadanda suke cikin ƴan jam’iyyar tara da suka dakatar da Ganduje kwanaki biyu da suka gabata.

Kotun ta kuma nemi Ganduje da ya daina ayyana kansa a matsayin mamba a jam’iyyar ta APC.

A baya-bayan nan ne wasu shugabannin APC tara a mazabar ta Ganduje suka ce sun dauki matakin dakatar da Ganduje bayan wata takardar koke da wani dan jam’iyyar Ja’afaru Adamu ya shigar.

A takardar koken, Adamu ya yi magana kan tuhume-tuhumen rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan inda ya bubaci jagororin mazabar su gudanar da bincike kan batun domin farfaɗo da kimar jam’iyyar.

Latest stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...

Related stories

Ƙungiyar Hamas ta isa birnin Al-Qahira game da tattaunawa kan tsagaita wuta.

Rahotanni daga kasar Masar, sun ce tawagar jami’an kungiyar...

An kashe ƴan ƙato da gora sama da 23 a Barno da Sakkwato.

Rahotanni daga jihohin Borno da Sakkwato sun ce, an...