Saurari premier Radio
37.3 C
Kano
Thursday, May 16, 2024
Saurari Premier Radio
HomeFIFAAbin da ya kamata ku sani kan Yunkurin Fara Amfani da Shudin...

Abin da ya kamata ku sani kan Yunkurin Fara Amfani da Shudin – Kati a kwallon Kafa

Date:

Hukumar da ke Kula da tsara dokokin kwallon kafa ta duniya IFAB ta ce, za ta tattaunawa batun fara amfani da shuÉ—in-kati (Blue Card) a wasannin Kwallon kafa.

Ana sanar hukumar ta IFAB za ta gudanar da babban taron ta na Shekara-shekara a cikin watan Maris mai zuwa a kasar Scotland.

Inda ake saran hukumar za ta Tattaunawa batun fara amfani da Shudin-Kati a yunkurin fara amfani da shi a wasannin League na kasashe.

Da zarar amfara amfani da Shudin-Katin, dan wasa zai kwashe minti 10 a wajen fili yana hutawa idan Alkalin wasa ya ba shi shuÉ—in katin.

A yanzu dai ana amfani ne da katuna biyu, wato kati mai ruwan É—orawa (Yellow card) a matsayin katin gargaÉ—i, da kuma jan kati (Red card) a matsayin katin kora da zarar mutum ya yi keta mai girma.

Dama dai ana amfani da shudin kati a wasannin kwallon kafa a mataki na kasa-kasa, sai dai ana sa ran kawo shi cikin manyan gasannin League domin fara amfani da shi.

To amma babu tabbacin ko yaushe za a fara gwajin shudin katin da kuma gasar da za a fara yin gwajin musamman a wasannin nahiyar turai.

Yanzu haka tuni gasar Firimiya ta Ingila ta kushe batun gwajin katin a wasanninta, yayin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce bai kamata a fara batun amfani da katin a manyan gasannin duniya ba a yanzu.

Dama wasu na ganin matakin kasar Ingila na kawar da batun ba abin mamaki bane, domin ko a Lokacin fara amfani da na’urar VAR kasar da fari ta kushe batun kafin daga bisani tayi mi’ara koma baya.

Latest stories

Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Malam Nuhu Ribadu.

Majalisar Dattawa ta gayyaci mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran...

Matar Shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan Na Ziyara Najeriya.

Uwargidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan na wata ziyara a...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...