Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMajalisar Dattawa Ta Gayyaci Malam Nuhu Ribadu.

Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Malam Nuhu Ribadu.

Date:

Majalisar Dattawa ta gayyaci mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran tsaro Malam Nuhu Ribadu, saboda lalacewar jiragen Fadar Shugaban Kasa.

Shugaban kwamitin lura da jiragen fadar shugaban a Majalisar, Sanata Satomi Ahmed, ne ya sanar da hakan.

Alhakin kula da jirgin shugaban kasa da mataimakinsa dai ya rataya ne a wuyan mai bai wa shugaban kasa shawara kan al’amuran tsaro.

Sanata Satomi Ahmed ya ce akwai kasafi na musamman domin kula da jiragen fadar shugaban kasa.

Ya ce wadannan makudan kudade suna karkashin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ne.

Ya kara da cewa akwai kaso mai tsoka na shekara-shekara daga Majalisar don kula da jiragen.

Satomi ya bayyana damuwarsa, da cewa abin kunya ne halin da jiragen shugaban kasar ke ciki.

Ya ba da misali da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da yadda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya shiga matsala sanadiyyar lalacewar jirgin, wanda dole sai dai ya yi amfani da jirgin haya domim tafiye-tafiye da suka shafi aikinsa.

Satomi ya ce ya kamata ace Kasar nan na iya kula da jiragenta, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da ta samu a baya kamar iya samar da kamfanin Nigeria Airways.

Latest stories

Related stories