Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaGwamnatin tarayya ta ce babu wani shirin kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar...

Gwamnatin tarayya ta ce babu wani shirin kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar Israila da Falasdin

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce babu wani shirin kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar Israila ko kuma Falasdin duk da ruwan bama-bamai da Isra’ilan ke kaiwa kan mazauna Gaza.
Ma’aikatar kula da ‘yan Nijeriya da ke kasashen ketare ce ta bayyana haka, inda ta ce ba ta samu wani kiran waya ba daga wani mutum ko kungiya na ‘yan Nijeriya da ke cikin barazana ba game da yakin da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Abdur-Rahman Balogun ya ce kasar nan za ta kwaso ‘yan Nijeriya ne kawai idan ta samu kiran waya daga ‘yan Nijeriyan da ke kasashen guda biyu, amma har yanzu ba ta samu hakan ba.
Dubban ‘yan kasashen waje ne suka makale a Isra’ila da kuma kasar Falasdin, inda ake gwabza kazamin yakin da ya kashe daruruwan mutane ciki har da kananan yara.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...