Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyoyin kwadagon kasarnan NLC , TUC da NECA sun koka kan yadda...

Kungiyoyin kwadagon kasarnan NLC , TUC da NECA sun koka kan yadda ake ci gaba da samun faduwar darajar Naira

Date:

Kungiyoyin kwadagon kasarnan NLC da TUC da kuma kungiyar tuntuba ta masu daukan ma’aikata, NECA, sun koka kan yadda ake ci gaba da samun faduwar darajar Naira, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa na daidaita lamarin.
Kungiyar ta NLC ta yi gargadin cewa idan ba a yi gaggawar daukar matakan da suka dace don tilastawa hukumomin da abin ya shafa ba wajen ceto darajar naira to hakan zai kara rusa tattalin arzikin kasar da kuma al’umar kasar baki daya.
A yayin da ita kuma kungiyar ta TUC ta bayyana damuwa kan illar da faduwar darajar Naira ke yi ga ma’aikata, ta hanyar hauhawar farashin kayayyaki, ita ma kungiyar NECA, wadda ita ce muryar kasuwanci a Najeriya, ta koka kan yadda faduwar darajar Nairar ya sa durkushewar kasuwanci a kasar.
Daga bisani kungiyoyin sun bukaci gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalolin da suka kawo faduwar darajar nairar domin magance matsalar hauhawar farashi da ake fuskanta a kasar.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...