Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba kasa Bola Tinubu, zai gabatar da kasafin kudin badi ga majalisun...

Shugaba kasa Bola Tinubu, zai gabatar da kasafin kudin badi ga majalisun dokokin kasar nan

Date:

Shugaba kasa Bola Tinubu, zai gabatar da kasafin kudin badi ga majalisun dokokin kasar nan da makonni biyu masu zuwa domin tantancewa.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa sanata Solomon Adeola, wanda ya bayyana haka a wajen taron kaddamar da kwamitin ya ce majalisar za ta tabbatar da cewa an zartar da kasafin kudin kafin karewar wannan shekarar.
Da yake magana kan jinkirin gabatar da kasafin kudin da shugaban kasar ya yi, Sanata Adeola, ya alakanta hakan da sauyin gwamnati a matsayin abu mai muhimmanci da ya kamata a yi la’akari da shi.
Shugaban kwamitin ya ce za su yi aiki sosai kan kasafin kudin kuma aikinsu ne tabbatar da kasafin kudin domin biyan bukatun jama’a.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...