Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar DSS ta saki Tsohon shugaban hukumar EFCC Abdurrashid Bawa

Hukumar DSS ta saki Tsohon shugaban hukumar EFCC Abdurrashid Bawa

Date:

Yadda iyalan tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, Abdulrashid Bawa suka tare shi cikin murna bayan da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sake shi.
Bawa dai ya shafe kwanaki 134 tsare a hannun DSS, tun lokacin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da shi daga mukaminshi a watan Yuni.
Gwamnatin Tinubu dai ta ce ta dakatar da shi ne saboda a samu damar gudanar da cikakken bincike kan zargin aikata almundahanar da ake yi masa.
Jaridar Daily Trust ta ce wata majiya daga jami’an tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida cewa an saki Bawa ne bayan fuskantar matsin lamba daga wasu masu karfin fada aji a cikin jami’an tsaron kasar nan.
Kazalika, wata majiyar ta ce an sake shi bayan hukumar ta DSS ta kammala bincikenta a kan shi.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...