Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano ta mika kwarya-kwaryan kasafin kudi na naira biliyan 58 ga...

Gwamnatin Kano ta mika kwarya-kwaryan kasafin kudi na naira biliyan 58 ga Majalisar dokoki

Date:

Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi kwarya kwaryar kasafin kudi na naira biliyan 58 daga gwamnan kano Abba Kabir Yusif.

Shugaban majalisar Isma’il Falgore ne ya bayyana karbar kasafin a jiya litinin, inda yace gwamnatin jihar na neman sahalewar majalisar kamar yadda sashe na 121 karamin sashe na A da B cikin baka na kundin tsarin mulki 1999 ya tanada.

Falgore yace gwamnatin tace aiwatar da kasafin a yanzu ya zama wajibi domin saita alkiblar ayyukan gwamnati wajen cimma burin da ta sa gaba na gabatar da muhimman ayyuka a wanna shekara.

An dage zaman majalisar zuwa yau Talata domin cigaba da tattauna batun.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...