Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar likitocin hakoran yara ta kasa ta ce kwararrun likitocin hakorin yara...

Kungiyar likitocin hakoran yara ta kasa ta ce kwararrun likitocin hakorin yara 84 ne kacal ake dasu a fadin kasar nan.

Date:

Kungiyar likitocin hakoran yara ta kasa ta ce kwararrun likitocin hakorin yara 84 ne kacal ake dasu a fadin kasar nan.

Shugabar kungiyar ta kasa Dr Ify Adegbulugbe ce ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta kafafen sada zumanta kan matsaloli da suka shafi fannin hakori a kasar nan.

Ta ce akwai kalubale da dama a fannin lafiya, musamman barin aiki zuwa kasashen waje da likitocin kasar keyi.

Da yake tsokaci kan wannan, shugaban kungiyar manyan likitoci ta kasa reshen Kano, Dr Mustapha Sa’idu Salihu ya ce bama iya likitocin hakori na yara ne ke karanci a kasar ba.

Mustapha Salihu ya kara da cewa za a iya magance matsalar karancin likitocin wajen samun karatu na kwarewa.

To sai dai ya ce ko a kasashen da suka cigaba ma ana karancin likitocin hakorin yara.

Kungiyoyin likitoci dai sun sha kokawa kan karancin likitoci a kasar nan, wanda suka alakanta hakan da gazawar gwamnatin na biyan hakkokin likitocin, hakan yasa suke guduwa kasashen waje domin aiki.

Latest stories

Related stories