Saurari premier Radio
24.7 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJamiyyar PDP ta zargi akwai ayar tambaya game da gobarar da ta...

Jamiyyar PDP ta zargi akwai ayar tambaya game da gobarar da ta tashi a ginin kotun kolin kasar nan

Date:

Jamiyyar Adawa ta PDP tayi Allah wadai da gobarar da ta tashi a wani bangare na ginin kotun kolin kasar na a safiyar jiya Litinin.

A wata sanawarwa da jamiyyar ta fitar a jiya Litinin, PDP tace akwai lauje cikin nadi, ganin cewa gobarar ka iya gurgunta shirin sauraran karar da jamiyyar ta shigar gaban kotun kolin inda take kalubalantar nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da ya gabata.

Sanarwar da sakataren labaran jamiyyar na kasa Debo Olugnaba ya sanyawa hannu, ta ce jamiyyar ta bukaci gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashin gobarar, sannan kuma a bayyanawa yan Najeriya sakamakon binciken maimakon yin rufa rufa kamar yadda aka saba.

A karshe sanarwar ta bukaci gwamnati ta tsaurara tsaro a harabar kotun  da bin bahasi kan halin da muhimman takardu da kayan aikin kotu ke ciki a halin yanzu.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...