Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNATCOM ta nesanta kanta da masu yaudarar alumma da sunan sama musu...

NATCOM ta nesanta kanta da masu yaudarar alumma da sunan sama musu aiki da hukumar

Date:

Hukumar yaki da yaduwar kananan makamai ta kasa NATCOM, ta ja hankalin al’umma kan su yi taka tsan-tsan da wasu batagari dake yaudarar jama’a da sunan samar musu aiki da ita.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin bincike da ladabtarwa na hukumar, Commondore Idris Jibrin Mai ritaya ya fitar a Juma’ar nan, ta ce mutanen na yin haka ne ba da yawunsu ba.

NATCOM ta shawarci al’umma, da su guji mu’amula da mutanen domin tuni ta dakatar da su sakamakon samun su da wasu laifuka a kwanakin baya.

A baya dai hukumar ta fuskanci rikicin shugabanci duk da zaman jira da take na tabbatar da ita a matsayin cikakkiyar hukuma, yayin da take jiran sanya hannun shugaban kasa bayan tsallake tantancewar majalisun kasar nan.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...