Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoKotu ta haramtawa Jami'an tsaro kama Ganduje

Kotu ta haramtawa Jami’an tsaro kama Ganduje

Date:

Kotu a nan Kano ta haramtawa jami’an tsaro kama tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Alhamis ne hukumar yaki da cin hanci ta jihar, ta aike da goron gayyata ga tsohon gwamnan, domin amsa tambayoyi kan faifan bidiyo da aka hango shi yana karbar cin hanci daga yan kwangila.

Tsohon gwamnan ne ya shigar da kara gaban kotun ta hannun lauyan sa Mr B. Hemba.

Mai shari’a A.M Liman yace matakin haramcin zai cigaba da wanzuwa har zuwa 14 ga watan Yuli da muke ciki, ranar da kotun zata saurari shari’ar.

Wadanda ake karar sun hadar da hukumar yan sanda, Sipetan yan sanda na kasa, babban lauyan gwamnatin tarayya, babban lauyan gwamnatin Kano, sai hukumar yaki da cin hanci ta Kano PCACC da kwamishinan yan sandan Kano, da hukumar tsaro ta farin kaya SSS, da kuma Rundunar tsaro ta farar hula NSCDC.

 

 

Latest stories

Related stories