Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeAl'aduYan kabilar Igbo mazauna Legas sunyi asarar miliyoyi sanadiyar harin da aka...

Yan kabilar Igbo mazauna Legas sunyi asarar miliyoyi sanadiyar harin da aka kai musu bayan zaben shugaban ƙasa

Date:

Hadakar jagororin kabilar Igbo karkashin gidauniyar kula da harkokin ‘yan kabilar sun bukaci Inyamuran da ke zaune a Lagos su kaucewa mayar da martani dangane da hare-haren da ake kai musu a sassan jihar.

Kungiyar ta kuma ce ganin yadda wannan al’amari ke ci gaba da tsananta tun bayan zaben shugaban kasa na watan Fabarairu, ya kamata kasashen duniya su dauki matakin shiga tsakani tun kafin abun ya juye zuwa rikicin kabilanci a wannan jiha mai tarin ‘yan kabilar Igbo da ke kasuwanci.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce dole ne gwamnatin jihar Lagos da takwararta ta tarayya su biya ‘yan kabilar ta diyyar dukiyar miliyoyi dangane da asarar da suka yi sakammakon hare-haren da ake kai musu.

A wani jawabi ga manema labarai a birnin Owerri a jihar Imo, shugaban kungiyar ta dattijan na Igbo, Bishop Maglorious Enyioha, ya ce ‘yan kabilar na fuskantar kyama a sassan jihar Lagos kawai saboda sun zabi son ransu.

Wannan kira na dattijan Igbo na zuwa kwana guda bayan kai hari kan shugaban majalisar dattijan kungiyar, Chief Emmanuel Iwuanyanwu, bayan wasu kalamai da ya alakanta Yarabawa da zama ‘yan jagaliyar siyasa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...