Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKarancin kudi:NLC za ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan

Karancin kudi:NLC za ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan

Date:

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC  ta umarci ma’aikata su fara zanga-zanga a dukkanin ofisoshin babban bankin ƙasar tun daga mako mai zuwa saboda ƙarancin takardun naira da ake fama da shi.

Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, wanda ya yi wa manema labarai a Abuja bayani game da shirin, ya ce daga jibi Juma’a ne za su fara haɗuwa sannan kuma su fara rufe dukkanin harkokin kasuwanci daga ranar Laraba mai zuwa a faɗin ƙasar.

A ranar 13 ga watan nan na Maris ne ƙungiyar ta NLC ta bai wa gwamanatin tarayya wa’adin kwana bakwai na ta ɗauki matakan sassauta matsalar da ake fama da ita ta ƙarancin takardun kuɗin naira da kuma ƙarancin mai, ko kuma ta kira yajin aiki na ma’aikata.

Shugaban ya ce, matakin zanga-zangar shi ne abu na ƙarshe da ƙungiyar za ta ɗauka kasancewar ta bi dukkanin matakan da ya kamata ta bi na ganin an samu sassauci kan tsananin wahalar da ma’aikata da sauran ƴan Najeriya ke sha saboda ƙarancin takardun kuɗin amma abin ya gagara

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...