Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zabe

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zabe

Date:

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ta ya  Abba Kabir Yusuf murnar lashe zaben gwamnan Kano da yayi.

Wannan kunshe cikin wata sanarwa da sakataren yada Labarai na Masarautar Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce al’ummar kasar nan sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matuqar muhimmacin idan akayi la’akari da yadda suka fito domin jefa kuri’unsu kamar yadda tsarin mulki ya bada dama.

Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al’umma bisa addu’ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.

Sarkin ya bukaci sabon gwamnan daya hada kai da dukkanin rukunin al’umma wajen tafiyar da gwamnatinsa

A cewarsa yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.

Alhaji Aminu Ado Bayero  yayi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano har ma da sauran sassan kasar nan.

yayi addu’ar fatan kammala tenure mulkinsa lafiya tareda samun cigaban gwamnatinsa da habaka tattalin arzikin jihar Kano.

Latest stories

Related stories