Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaYadda aka bude gadar Lado bayan shafe sama da watanni 6 a...

Yadda aka bude gadar Lado bayan shafe sama da watanni 6 a rufe.

Date:

Akalla sama da watanni biyar da rufe gadar Ado Bayero wadda akafi sani da Gadar Lado, hukumomi sun sake bude gadar.

 

Wannan ya biyo bayan fashewa da wani bari na gadar ya yi, wanda ya janyo hukumomi suka rufeta.

 

Alumma sai sun sha fama bisa rufe hannu daya na gadar, inda akayita samun cinkoso na ababen hawa ba kakkautawa.

Karamin ministan ayyauka da gidaje Hon. Umar Ibrahim El-Yakub ne ya jagoranci bude gadar sakamakon gyara da akayi mata.

 

Ibrahim El-Yakub ya ce gyara da akayi ingantacce ne zai taimaka wurin kare duk wata barazana ga masu bin gadar saman.

 

Ya kuma yi alkawarin cewa za’a sake zuba sabuwar kwalta a daya bangaren na gadar don kara inganta ta.

 

Daga bisani karamin ministan ayyukan Ibrahim El-Yakub yayi kira ga al’ummar jahar Kano dasu kara sanya idanu akan duk wasu bata gari dake lalata kadarorin gwamnati domin kaucewa sake faruwar hakan anan gaba.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...