Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari zai tafi Mauritania don karbar kyautar zaman lafiya

Buhari zai tafi Mauritania don karbar kyautar zaman lafiya

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari  zai tafi kasar Mauritania don karbar kyautar zaman lafiya.

 

Mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace shugaban kasar zai karbi kyautar saboda irin gudunmawar da yake baiwa ta fannin zaman lafiya a Afirka.

 

Buhari zai karbi kyautar Karfafa zaman lafiya ne a kasar

 

Adesina ya ce kafin karbar kyautar zaman lafiyar, Buhari zai gabatar da makala a taron Afirka kan samar da zaman lafiya.

 

Ya kuma kara da cewa Buhari zai bar kasar nan a yau Litinin.

 

A cikin tawagar da zata raka shugaban kasa Muhammadu Buhari akwai ministan harkokin wajen kasar nan, Geoffrey Onyeama da minisan Tsaro Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar nan Ahmed Rufai Abubakar da sauransu.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...