Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan bindiga sunyi garkuwa da mutane 25 suna tsaka da ibada a...

Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 25 suna tsaka da ibada a Katsina.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Rahotanni daga jihar Katsina na tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan wata coci dake karamar hukumar Kankara tare da sace mutane 25 suna tsaka da ibada.

 

Mai baiwa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari shawara kan batutuwan dake da alaka da mabiya addinin kirista  Rabaran Ishaya Jurau  ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Buhari zai tafi Mauritania don karbar kyautar zaman lafiya

Yadda yan bijilanti suka fasawa wata amarya ido saboda kidan DJ a Kano.

 

Rabaran Ishaya Jurau ya ce cocin da yan bindigar suka kaiwa harin tana unguwar Jan-Tsauni ne a karamar hukumar kankara.

 

Sai dai Faston cocin ya tsallake rijiya da baya amma ya gamu da raunuka yayin harin.

 

Ya kara da cewa an kai harin ne ranar Lahadi, lokacin da mutanen suke tsaka da ibada a cocin.

 

Jaridar Thisday ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da karfe 10:00 na safe.

 

 

Latest stories

Related stories