Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaYadda yan bijilanti suka fasawa wata amarya ido saboda kidan DJ a...

Yadda yan bijilanti suka fasawa wata amarya ido saboda kidan DJ a Kano.

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

 

Ana zargin wasu jami’an sa kai na bijilanti da fasawa wata Amarya Khadija Abdullahi ido tare da cin zarafinta saboda tayi kidan DJ a bikinta.

 

 

Lamarin ya faru ne a unguwar Kwajalawa, Dan-tamashe da ke  Rimin Kebe a karamar hukumar Ungoggo.

 

 

Amarya Khadija Abdullahi, ta ce suna tsaka da biki ne a cikin unguwa,  yan bijilanti su kimanin 10 suka isa wurin, kuma suka tarwatsa taron bikin nasu.

 

 

Ta kuma ce tana fatan mahukunta za su bi musu hakkinsu tare da yi musu adalci, ta hanyar hukunta wadannan yan bijilanti na garin kwajalawa.

 

 

A cewar mahaifin amaryar Malam Abdullahi Mu’azu ya damu sosai saboda yadda aka mayar da ranar farin cikinshi da yarsa zuwa ranar bakin ciki.

 

 

Malam Abdullahi ya ce shi mai karamin karfi ne don haka yana fata, tare da rokon hukumomi za su dubi lamarin su kwato masa hakkin yar tasa.

 

 

Wata da hatsaniyar ta faru a kan idonta mai suna Hajara, ta ce ‘yan kwamitin da makamai suka je wurin tare da dukan jama’a kan mai uwa da wabi.

 

 

Da yake martini kan lamarin shugaban Bijilanti na jihar Kano Shehu Rabi’u ya tabbatar da cewa wadanda sukayi aika-aikar jami’an bijilantine, sai dai ba mambobinsu bane.

 

 

Sai dai a lokacin da yake wannan musantawa al’umma na tabbatar da cewa jami’an bijilantine suka aikata wannan aika-aika.

 

 

Latest stories

Related stories