Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiInada kwarin gwiwa kan na’urar dakile magudin zabe ta BVAS da INEC...

Inada kwarin gwiwa kan na’urar dakile magudin zabe ta BVAS da INEC ta samar –Kwankwaso

Date:

Mukhtar Yahaya Usman

 

 

Dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce gamsu da a yi amfani da na’urorin da za su hana magudin zabe.

 

 

Kwankwason ya bayyana hakan ne ya yin taron gangamin kaddamar da takararsa da kuma baiwa yan takarar jam’iyyar tuta a jihar Kaduna.

 

 

Sanata Kwankwaso ya ce abun da ke kara mai kwarin gwiwa game da zaben wannan shekarar shi ne amincewa da amfani da na’urar BVAS da zata taimaka wajen hana magudin zabe.

 

 

Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali, shi ne shugaban Jam’iyyar NNPP a Najeriya, ya ce al’umma su ne alkalan kansu game da halin da kasar nan ke ciki.

 

 

Shi kuwa jigon Jam’iyyar ta NNPP, Alh. Buba Galadima cewa ya yi a wannan lokaci da ake tunkarar babbn zaben 2023 yakamata al’ummar yankin arewa maso yamma su shiga taitayinsu.

 

 

Tun bayan da INEC ta ce zatayi amfani da wannan na’ura ta BVAS don dakile magudin zabe dai alumma suke tofa albarkacin bakinsu, inda galibin jama’a suke ganin idan har anyi amfani da na’urar yadda yakamata to baba shakka zata dakile magudi a zaben 2023 dake tafe.

Latest stories

Related stories