Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar NIS reshen Kano ta yaye jami’ai kusan 2000

Hukumar NIS reshen Kano ta yaye jami’ai kusan 2000

Date:

Abdurrashid Hussain

 

Hukumar kula da shige da fice ta kasa NIS, reshen jihar Kano, ta yaye jami’ai dubu daya da dari takwas daga kwalejin horar da jami’anta da ke nan Kano.

 

NIS ta ce Jami’an da aka yaye a Asabar dinnan, sun hadar da wadanda da suka yi kwas na 2.

 

Shugaban hukumar, Isah Jere Idris, da ke taya murna ga wadanda aka yaye, tare da yin kira gare su, kan su yi aiki da horon da suka samu bisa bin dokoki da ka’idojin aiki na hukumar.

 

Isah Jere wanda mataimakinsa, mai kula da sha’anin ma’aikata, Babangida Usman ya wakilta, tare da duba faretin wadanda aka yaye din .

 

Ya bayyana cewa, hukumar na ci gaba da aiki wajen inganta sha’anin jami’anta, ta hanyar basu horo, domin su iya fuskantar kalubalen da ke tasowa a bangaren kula da tsaron iyakokin kasa da harkar shige da fice.

 

Ya kuma nanata bukatar da ake da akwai ga jami’an, kan su kaucewa yin sakaci da zubar da mutuncin aiki, musamman a yanzu da ake fuskantar zaben 2023.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...