Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKamfanin Shell zai biya manoman Neja- Delta diyyar Dola Miliyan 16

Kamfanin Shell zai biya manoman Neja- Delta diyyar Dola Miliyan 16

Date:

Hafsat Nasir Umar

 

Kamfanin hakar danyen man fetur na Shell zai biya diyyar dala miliyan 16 ga wasu manoma a yankin Neja-Delta.

 

Hakan na cikin diyyar da kamfani zai biya ga waÉ—anda malalar man fetur ta yi musu barna a gonakinsu.

 

Alkawarin biyan diyyar na kunshe cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a tare da hadin gwiwar reshen cibiyar Friends of the Earth a kasar Netherlands.

 

Matakin ya biyo bayan hukuncin kotun Netherlands inda ta kama reshen kamfanin na Shell a Najeriya da laifin malalar mai a shekarar da ta wuce kuma ta umarci Shell ya biya diyya.

 

Tun a shekarar 2008 ne manoma daga Neja-Delta tare da taimakon kungiyar kare hakkin bil adama ta Friends of the Earth suka gurfanar da Shell a gaban kotun da ke The Hague sakamakon gurbata musu muhalli da ya yi a tsawon shekarun da ya shafe yana hako albarkatun fetur a yankin.

 

Kamfanin Shell ya yi barnar a shekarun 2004 zuwa 2007.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...