Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan Majalisa sun ci alwashin dakatar da kudurin takaita cirar kudi na...

Yan Majalisa sun ci alwashin dakatar da kudurin takaita cirar kudi na CBN

Date:

Hafsat Nasir Umar

‘Yan Majalisar Wakilai sun ci alwashin tilasata wa Babban Bankin kasa (CBN) dakatar da shirin takaita adadin kudin da ‘yan kasa da kamfanoni zasu cira a kullum.

 

Wani daga cikin shugabanni a Majalisar ya shedawa jaridar daily trust cewa akasarinsu sun aminta cewa ya kamata a jingine dokar baki dayanta.

 

A cikin sabuwar dokar, mafi yawan abin da mutum zai iya cirewa a mako na tsabar kudi shi ne naira N100,000, kamfani kuma N500,000. Daga baya aka kara adadin zuwa N500,000 ga mutane da kuma 5,000,000 ga kamfanoni.

 

Tun da farko Majalisar ta nemi CBN ya jinkirta fara amfani da dokar, wadda za ta fara aiki daga 9 ga watan Janairun 2023, har sai gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana a gabanta.

 

Sai dai Mista Emefiele bai amsa gayyatar ba yana mai cewa ya fita kasar waje don a duba lafiyarsa.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...